Za a yi taron na birnin Hangzhou ne a ranekun 4 da 5 ga watan Satumbar bana, kuma tun shekarar da ta gabata birnin Hangzhou ya fara shiri gabanin zuwan taron, inda ya tsara shirye-shirye kimanin 651 domin kyautata muhallin birnin, da inganta ababen sufuri, da kuma ayyukan dake shafar harkokin dakunan taro, da otel da dai sauransu. Haka kuma a halin yanzu, ana ci gaba da inganta ayyukan da suka shafi shirye-shiryen.
Bugu da kari, aikin kiyaye tsaro shi ne mafi muhimmanci wajen gudanarwar taron, don haka birnin Hangzhou ya aiwatar da manyan manufofin musamman guda goma, domin kyautata harkokin tsaron birnin. Ban da haka kuma, ana ci gaba da samun karin mazauna birnin na Hangzhou wadanda ke shiga ayyukan ba da hidima, da kiyaye tsaro domin nasarar taron kolin kungiyar ta G20.
Babban makasudin taron kungiyar G20n shi ne ciyar da shawarwari da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu ci gaba, da kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki gaba, ta yadda za iya inganta zaman karko a sha'anin kudin kasa da kasa, da kuma ci gaba na bunkasuwar tattalin arzikinsu.
A halin yanzu, kasashe mambobin kungiyar G20 su ashirin, wadanda suka hada da kasashen Amurka, Jamus, Rasha, Brazil, Sin da dai sauransu. Kuma GDPn wadannan kasashe gaba daya ya kai kashi 90 bisa dari na dukkanin GDPn kasashen duniya. Kaza lika karfin cinikayyarsu ya kai kashi 80 bisa dari na duk duniya. (Maryam)