Wang Yi ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya a wannan rana game da taron kolin G20 na Hangzhou.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, saboda haka ta fahimci muhimmancin bunkasuwa sosai. An zabi kasar Sin domin shirya taron kolin G20, don haka ya dace a sanya batun bunkasuwa a muhimmin matsayi, kuma wannan fatan ne na kasashe masu tasowa baki daya, kana nauyi ne da ya kamata kasar Sin ta dauka. (Bilkisu)