Wadannan nasarori 10 da za a yi kokarin cimmawa sun hada da tsara shirin samun ci gaba ta fannin kirkire-kirkire, da shirin ayyukan ajandar samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030, da fannonin da aka baiwa muhimmanci yayin da ake yin kwaskwarima kan tsari, da ka'idojin ba da jagoranci, da manufofin sa kaimi ga bunkasuwar cinikayya a duniya, da ka'idojin ba da jagoranci ga manufofin zuba jari a duniya, da zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin hada-hadar kudi na duniya, da yin hadin gwiwa a yaki da cin hanci da rashawa, da gabatar da shawarar hadin kai don nuna goyon baya ga kasashen Afirka da kasashe marasa samun ci gaba wajen raya masana'antu. Wadannan kasashe suna bukatar a gaggauta raya masana'antunsu, da kara karfin raya kasu da kansu. A shekarar bana, kasar Sin za ta sa kaimi ga membobin kungiyar G20 da su yi hadin gwiwa, da taimakawa kasashen wajen gaggauta raya masana'antunsu da rage talauci da cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa ta hanyar inganta karfi, kara zuba jari, kyautata ayyukan more rayuwa da sauransu.
Hakazalika kuma, za a tsara shirin da zai taimaka wajen kafa kamfanoni, da gaggauta aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris game da sauyin yanayi. (Zainab)