A ganin madam Ramos, Sin ta nuna wa kungiyar G20 sabbin manufofi uku da ta dora muhimmanci a kai. Na farko shi ne yin kirkire-kikire. Ta ce, Sin ta gabatar da manufar samun ci gaba bisa tushen yin kirkire-kirkire, wadda ta zama aikin sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki na kasa da kasa, da kuma farfado da bunkasuwar tattalin arzikin duniya a dogon lokaci.
Na biyu shi ne samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Ramos ta bayyana cewa Sin tana kokarin kara zuba jari ga makamashin da za a sake yin amfani da shi, da daukar matakan don kyautata yanayi, shawo kan kiyaye muhalli, wadanda suka samu karbuwa sosai a duniya.
Na uku shi ne gudanar da tattaunawa a hakika. (Zainab)