--Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai dawo gida daga London inda ya kwashe kwanaki 10 yana jinyar ciwon kunnen da ya ke fama da ita ne a ranar Lahadi.
Yemi Osibanjo ya shaidawa wakilan kafofin watsa labarai da ke fadar shugaban kasa hakan ne a jiya Alhamis jim kadan kafin fara taron majalisar tattalin arzikin ta kasa da ya gudana a fadar shugaban kasar da ke Abuja,fadar mulkin Najeriya.(The Punch)
--A jiya ne hukumar EFCC da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta damke tsohon shugaban hukumar kwastan na kasar Abdullahi Dikko Inde, bisa zargin da ake masa na almundahanar kudade.(Daily Trust)