Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa Othman Abubakar ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua da ke Yola, fadar mulkin jihar cewa, harin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare agogon wurin.
Kakakin 'yan sanda ya kuma tabbatar da cewa,'yan sanda sun yi nasara damke wani da ake zaton mayakin Boko Haram ne a garin Gombi da ke jihar ta Adamawa.(Ibrahim)