Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ta fasa bututun man ne da misalin karfe 4 na safiyar yau agogon kasar.
Fasa bututun man na zuwa ne sa'o'I 72 bayan da kungiyar ta zayyana wasu ka'idoji kafin ta shiga tattaunawa da bangaren mahukuntan kasar ta Najeriya.(Ibrahim)