Bayan kammala aikin, za a tsawaita hanyar saukar jiragen sama da tsawon mita 500, ta yadda manyan jiragen sama na kasar, za su iya sauka ba tare da matsala ba. Rahotanni na cewa, yawan kudin kwangila ya kai dalar Amurka miliyan 68, kuma za a shafe watanni 12 ana wannan gyara.
A yayin bikin, Ministan Gnofam ya ce, filin jiragen sama na Niamtougou ya kasance wani muhimmin filin jiragen sama dake yankin arewacin kasar Togo, gwamnatin Sin da bankin EXIM na Sin suna daga cikin wadanda suka dauki nauyin wannan aiki, bayan da aka gyara shi, zai kuma kyautata yanayin sufuri da ake ciki a yankin Kara da sauran wurare, da raya tattalin arziki da yawon shakatawa a arewacin kasar.(Bako)