in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki da ta'addanci: Ana sa ran zuwan kasashe tara a Lome domin tattauna batun kananan makamai
2016-02-10 11:40:44 cri
Kasashen yankin Sahel tara ne aka sa ran za su halarci daga ranar 10 zuwa 11 da watan Febrairu a birnin Lome na kasar Togo, wani taron karawa juna sani na amincewar shiyya da "bincike kan kananan makamai da nau'o'in kananan makamai (ALPC) a Sahel". Bisa shiryawar cibiyar shiyya ta MDD domin tabbatar da zaman lafiya da karbe makamai a nahiyar Afrika (UNREC), taron karawa juna sanin zai hada wakilan kasashe tara wato Burkina Faso, Kamaru, Afrika ta Tsakiya, Mali, Mauritaniya, Nijar, Nijeriya, Senegal da kuma Chadi. Kwararrun da suka halarci rubuta rahoton bincike, da ma wakilan cibiyoyin PNUD dake cikin kasashen da abin ya shafa su ma za su halarci wannan haduwa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China