Sai dai kakakin ya bayyana cewa a lokacin arangamar an kashe sojoji 7 bayan nasarar da suka yi a kan 'yan ta'addan sannan aka raunata sojoji 8.
Sojin Najeriyan ta bayyana cewa bayan dakile 'yan kungiyar sun kwato makamai masu yawan gaske da albarusai da sauran kayuayyaki da suka hada da bindiga komai da ruwan ka babba guda daya, da harsasin harbar roka guda biyu, da bindigar AK47 mai daure da harsasan NATO duk daga hannun 'yan ta'adda.
Makonni biyu da suka wuce fiye da 'yan ta'addan 200 suka mika wuya ga sojin kasar a garin Banki wani muhimmin garin da a baya 'yan ta'addan suka mamaye. Sojin na bayanin cewa sun hargitsa 'yan ta'addan a garuruwa da dama da unguwanni a jihohin Borno, Yobe da Adamawa duk a makonnin baya.
A wani labarin kuma sojojin kasar ta Nigeriya a Bama da Ngurosoye dake kusa da jihar ta Borno sun gano tare da hako wassu ababen fashewa da kungiyar ta boko haram suka binne, kamar yadda cibiyar tsaron kasar ta tabbatar.(Fatimah Jibril)