Cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Ban ya gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, sannan ya nuna goyon baya ga gwamnatin Amurka.
Wasu 'yan bindiga ne dai dauke da makamai suka bude wuta a wani wurin shakatawa a Orlando tun a farkon ranar Lahadi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 50.
Shugaba Barak Obama ya bayyana harin a matsayin hari mafi muni da ya hallaka jama'a a Amurka, inda ya bayyana shi a matsayin aikin 'yan ta'adda.
Wani kamfanin dillanci labaru na Amaq ya bayyana cewar mayakan kungiyar IS ne suka kaddamar da harin. (Ahmad Fagam)