Ministar ta bayyana hakan ne ga manema labaru a Abuja, a lokacin taron masu ruwa da tsaki a fannin, ta ce ma'aikatar za ta kafa kwamitin kwararru a makon gobe domin su samar da wani rubutaccen tsari don tunkarar matsalar.
Ta ce asali ma, an shirya taron ne da nufin nazarin hanyoyin da za'a bi don kawo karshen matsalar karancin tumatir da kasar ke fuskanta sakamakon barkewar annobar kwari dake lalata tumatir a sassan kasar.
Aisha ta ce kwamitin kwararrun wanda zai fara aiki a makon gobe zai samar da wani tsari don daukar matakai cikin hanzari gabanin fara noman tumatir na shekara mai zuwa.
Masu ruwa da tsaki a harkar tumatir da suka hada da manoma da masu sarrafa shi da wakilan hukumomin da ma'aikatu da abin ya shafa ne suka halarci taron. (Ahmad Fagam)