Ko da yake kwararru kan harkokin kudi a ciki da wajen kasar wadanda suka yi maraba da wannan tsari, sun bayyana cewa, tsarin tamkar karya darajar kudin kasar ne a fakaice. (Daily Trust)
--A yau ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai dawo gida daga London,bayan da aka canja lokacin da shugaban ya kamata ya dawo daga jinyar ciwon kunnen da ya je.(The Punch)
--An fuskanci zaman dar-dar a sakatariyar jam'iyyar adawa ta PDP da ke Abuja, fadar mulkin Najeriya, lokacin da wasu kungoyin matasa da ke gwagwarmayar neman karbe iko da sakatariyar suka doshi wurin.(The Guardian)