Bugu da kari, kasashen biyu sun zayyana matakan kara bunkasa sabon hadin gwiwar tasu a fannoni kamar amincewa da juna ta fannin siyasa, da shirin nan na tattalin arziki na siliki, da tsaron kasa da na shiyya, da al'adu da musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu da hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa.
Wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin biyu suka bayar bayan ganawar ta su, ta bayyana cewa, kasashen biyu sun amince su daga matsayin hadin gwiwar da ke tsakaninsu sakamakon nasarar da suka cimma ta fannin tattaunawa tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, amincewa da juna ta fannin siyasa da samun moriyar juna, tun lokacin da suka kulla irin dangantakar tsakaninsu a shekarar 2012.
A yayin da shugaba Xi na kasar Sin ya ke ziyarar aiki a kasar Uzbekistan, ana kuma saran zai halarci taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 16, wanda za a gudanar daga ranar 23 zuwa 24 ga wata.
Kasar Uzbekistan dai shi ne zango na uku kuma na karshe a rangadin da shugaba Xi ya kai kasashe uku, inda ya zuwa yanzu ya ziyarci kasashen Serbia da kuma Poland.(Ibrahim)