A yayin jawabinsa, shugaba Xi ya nuna cewa, a cikin shekaru 3 da suka wuce bayan da aka gabatar da shirin "Ziri daya da hanya daya", ko shakka babu wannan shiri ya samu karbuwa sosai daga kasashen dake kan hanyar, kuma an samu ci gaba sosai. Wannan ya nuna cewa, ana bin ra'ayin yin koyi da juna da neman moriya tare da samun nasara tare, tare kuma da tsaya kan manufar hada kai cikin lumana, da bude kofa ga kasashen ketare. Xi ya kara da cewa, akwai bambanci dake kasancewa tsakanin kasashen da shirin "Ziri daya da hanya daya" ya shafa a fannonin yanayin kasa da matsayin bunkasuwar tattalin arziki da kuma al'adu. Saboda haka, dole ne su nuna girmama ga juna da yi hakuri ga juna, kuma dole ne su taimaka wa wadanda ke fama da talauci don samun bunkasuwa cikin daidaici. Shirin nan aikin bai daya ne na kasashen, don haka akwai bukatar su yi kokari tare don neman hadin kai, da samu ci gaba.
Bayan haka kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasarsa na da niyyar da kuma kwarewa wajen tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arzikinta yadda ya kamata, yana kuma maraba da kasashe daban daban da su samu moriya sakamakon haka. (Bilkisu)