A jiya Talata, kafin ya fara ziyarar aiki a kasar Uzbekistan da kuma halartar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 16, shugaban kasar Sin ya bayar da sharhi mai taken bude sabon babin sada zumunta a tsakanin Sin da Uzbekistan ta kafofin yada labarai na kasar ta Uzbekistan, inda ya darajanta huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Har wa yau, ya ce, shekarar bana ita ce ta cika shekaru 15 da kafuwar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, don haka, kasar Sin tana fatan hada kan kasar Uzbekistan da ma sauran kasashe mambobin kungiyar, wajen daukaka hadin gwiwar da ke tsakaninsu bisa taron kolin kungiyar da za a gudanar, ta yadda kungiyar za ta kara amfana wa shiyyar da ma jama'ar kasashen.(Lubabatu)