Tusk ya bayyana a gun taron manema labaru bayan ganawarsa tare da firaminsitan kasar Potugal Antonio Maria Costa cewa, zai girmama duk irin sakamakon zaben jin ra'ayoyin jama'a a kasar Birtaniya da za a samu. Amma ya bayyana cewa, idan kasar Birtaniya ta janye daga kungiyar EU, hakan zai kawo illa ga nahiyar Turai har ma dukkan kasashen yammacin duniya.
Kana Tusk ya bayyana cewa, idan aka nuna goyon baya ga kasar Birtaniya da ta janye daga kungiyar EU, za a sa kaimi ga wasu kasashen da suka nuna shakku ga kungiyar EU da su janye daga kungiyar. Wannan zai zama mataki na farko na wargaza kungiyar EU.
A nasa bangare, Costa ya bayyana a gun taron manema labarum cewa, kasar Birtaniya tana da muhimmanci ga kungiyar EU, yana fatan kasar Birtaniya za ta ci gaba da zama memban kungiyar EU kamar yadda kasar Portugal ta yi. (Zainab)