Sakataren kudi na kasar Birtaniya George Osborne ya sanar jiya Talata cewar Birtaniya na shirin saka jarin da ya kai na Fam biliyan 1.9 don yaki da satar bayanai kan Intanet a cikin shekaru biyar masu zuwa, a kokarin hana 'yan ta'adda yin amfani da Intanet wajen kawo barazana ga tsaron kasar.
Mr. Osborne ya kuma kara da cewa, kungiyar IS mai tsattauran ra'ayi na yada munanan bayanan ta'addanci da tsara ayyukan ta'addanci ta Intanet. Hakan ana iya ganin cewa, Intanet ya kasance wani muhimmin bangare ko da yake ba shi da wani tasiri a fannin tsaron kasa da lafiyar jama'a a halin yanzu. (Kande Gao)