Hammond ya bayyana wa 'yan jaridar kasar Birtaniya cewa, bisa yanayi na rashin tabbas da ake fama da shi a kasar Libya, gwamnatin Birtaniya ba za ta kawar da yiwuwar daukar wannan mataki ba.
Hammond na ganin gwamnatin Libya ba ta bukatar taimako a fannin aikin soja daga kasashen waje, sai dai fa idan har kungiyar IS ta samu bunkasa a kasar, za ta haifar da barazana ga dukkan nahiyar Turai.
Kafin hakan, Italiya, Faransa, Jamus da sauran kasashe sun nuna goyon baya ga sabuwar gwannatin hadin kan al'ummar kasar Libya, suna fatan gwamnatin za ta nemi goyon baya daga kasashen waje, don yaki da kungiyar IS, da warware rikicin 'yan gudun hijira, da ci gaba da hako danyan mai, don farfado da tattalin arzikin kasar. (Zainab)