Firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya yi jawabi a birnin Bristol dake kudu maso yammacin Ingila a wannan rana da safe, inda ya bayyana cewa, idan kasar ta janye daga kungiyar EU, kasar za ta fuskanci babbar hasara. Kana sauran kasashen Turai za su ci gaba da yin tattaunawa da tsara kudurori, wadanda za su kawo babban tasiri ga kasar Birtaniya, sai dai ba za su tattauna tare da kasar Birtaniya kafin tsaida kudurinsu ba.
Muhimmin mutum daga cikin masu neman ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai (EU) kana tsohon magajin garin birnin London Boris Johnson ya halarci bikin neman samun goyon baya a wannan rana a birnin London. Ya bayyana cewa, yanzu kasar Birtaniya tana cikin wani muhimmin lokaci, kamata ya yi jama'ar kasar su nuna adawa da tsarin kungiyar EU. A cikin shekarun da suka gabata, tabarbarewar tattalin arzikin kungiyar EU ta kawo babbar illa ga kasar Birtaniya, yanzu lokacin ya yi da kasar ta janye daga kungiyar.
Bisa kididdigar da hukumomin binciken ra'ayoyin jama'ar kasar suka yi, jaridar Financial Times ta kasar ta nuna cewa, yawan mutanen da suka nuna goyon baya ga janyewa daga kungiyar EU ya kai kashi 45 cikin dari, wanda ya wuce na masu goyon bayan kasancewar Ingila a kungiyar da kashi 1 cikin dari. Don haka, jama'ar da ba su tsaida kuduri za su kawo babban tasiri ga sakamakon zaben jin ra'ayoyin jama'a na wannan karo. (Zainab)