in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Birtaniya zai zayyana sharuddan ci gaba da kasancewar kasar sa a tarayyar Turai
2015-11-09 09:47:38 cri
Nan da 'yan kwanaki ne ake sa ran firaministan kasar Birtaniya David Cameroon, zai zayyana sharuddan ci gaba da kasancewar kasar sa karkashin kungiyar tarayyar Turai.

Wasu rahotanni sun shaida cewa cikin mako mai zuwa Cameroon, zai lasafta dukkanin sharuddan kasar ta sa, cikin wata wasika da zai aike ga shugaban majalissar zartaswar kungiyar ta EU Donald Tusk.

A daya bangaren kuma firaminista Cameroon zai gabatar da jawabin musamman game da burin kasar sa na samun amincewar kungiyar ta EU game da wadannan bukatu.

Kaza lika Cameroon zai yi tsokaci game da dalilan masu fatan ficewar Birtaniya daga EU, dama na masu fatan akasin hakan. Cikin hadda tasirin ficewar ta a fannin tattalin arziki da kuma tsaro.

A jiya Lahadi ne dai sakataren wajen kasar ta Birtaniya Philip Hammond, ya shaidawa BBC cewa al'ummar kasar sa za su zabi ficewa daga kungiyar ta EU, muddin aka ki amincewa a gudanar da muhimman sauye-sauye. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China