Kakakin babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya fidda wata sanarwa a jiya Litinin, inda ya yi Allah wadai da jerin hare-haren ta'addanci da aka kai wa yankunan arewa maso yammacin kasar Syria wadanda ke bakin teku, ya kuma kalubalanci bangarori daban daban da su martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin kare rayukan al'ummar.
Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya fidda wani labari a jiya Litinin, wanda ke cewa, an kai hare-haren boma-bomai sau da dama a yankunan arewa maso yammacin kasar dake bakin teku, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 65. An kuma ce, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren na biranen Tartous da Jableh.(Lami)