in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zargi ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD a CAR da yin wassu sabbin ayyukan cin zarafi har 4
2016-02-17 11:07:54 cri
MDD a ranar talatan nan ta fitar da sabbin zargin har guda 4 na cin zarafi da ma'aikatan wanzar da zaman lafiyar majalissar suka yi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya. Sabbin zargin har 4 sun shafi ma'aikatan wanzar da zaman lafiya daga kasar jamhuriyar demokradiya ta Kongo, inji Farhan Haqq mataimakin Kakakin majailissar a ganawar da yayi da manema labarai, yana mai bayanin cewa rahoton farko da aka samu daga ofishin majalissar na MINUSMA dake CAR kungiyoyin sa kai ne suka gabatar a ranar 11 ga watan nan na Fabrairu.

Wadanda tsautsayin ya rutsa da su dukkan su kanann yara ne kuma mazauna sansanin Ngakobo wadanda suka rasa gidajen su dake Ouaka kuma an tabbatar da cewar ma'aikatan sun ci zarafin su tsakanin shekara ta 2014 da 2015.

A cewar Mr Haq ofishin manzar da zaman lafiyar na aiki tare da sauran hukumomin MDD da abokan huldar su domin tabbatar da cewar wadanda hakan ya faru da su sun samu ingantaccen kulawa kan lafiyar su da kuma tunanin su. Ya ce wadannan zargin ya biyo bayan cikakkun ayyukan da ofishin MINUSMA da hukumomin MDD keyi tare da mazauna domin bada kwarin gwiwwa ga wadanda tsautsayin ya ritsa da su su fito cikin mutane.

An sanar da kasashen da ake zargin Ma'aikatan nasu a ranar talatan nan tare da son su bayyana cikin kwanaki 10 aniyar su na binciken lamarin wanda gazawan hakan zai sa MDD ta aiwatar da nata binciken inji Mr Haq.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China