Yayin ganawar tasu, shugaba Xi Jinping da Andrzej Duda sun waiwayi zumuncin gargajiya da ya kasance tsakanin kasashen 2, gami da tsara hanyoyin da za a bi don kara dankon zumunta.
A cewar shugaba Xi, manufar ziyarar tasa ita ce samun karin fahimtar juna da amincewa da juna, da ingiza hadin gwiwar a tsakaninsu ta fuskoki da dama. Kasancewar kasar Poland na daya daga cikin mambobin kungiyar kasashen Turai EU, kuma kasar da ta fi karfin tattalin arziki a tsakiyar da gabashin nahiyar Turai, hakan ya sa kasar Sin ke neman hadin kai tare da kasar, don karfafa huldar dake tsakanin ta da kasashen da ke wannan yanki, gami da kasashen Turai baki daya.
A nasa bangare, shugaba Duda na kasar Poland ya ce, ya taba kai ziyara a kasar Sin a bara, inda babban ci gaban da kasar ta samu a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma ya burge shi kwarai da gaske. Haka kuma idan an dubi hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2 a shekarun baya, za a fahimci nasarori masu yawa. Don haka ya yi imanin cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasar Poland a wannan karo zai daga matsayin huldar dake tsakanin kasashen 2. Kana kasar Poland, bisa matsayinta na daya daga cikin mambobin jerin farko na bankin zuba jari a nahiyar Asiya mai kula da aikin gina ababen more rayuwa, tana son halartar kokarin da ake na gudanar da shirin 'ziri daya da hanya daya', gami da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2, musamman ma a fannonin gina kayayyakin more rayuwar jama'a, da shimfida layin dogo, da jigilar kayayyaki da makamantansu.(Bello Wang)