Jiya Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Serbia, Tomislav Nikolic a birnin Belgrade, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da wasu batutuwan dake janyo hankulansu, haka kuma, bayan shawarwarin dake tsakaninsu, shugabannin kasashen biyu sun cimma ra'ayi daya cewa, ya kamata a daga dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Serbia zuwa dangantakar abokantaka irin ta manyan tsare-tsare da kuma bisa dukkan fannoni, domin bude wani sabon shafi ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kaza lika, a yayin ganawar shugabannin biyu, Mr. Nikolic ya mika lamba mafi daraja na kasarsa ga Xi Jinping, watau "lambar nuna girmamawa ta matsayin farko ta jamhuriyar kasar" domin nuna masa godiya kan kokarin da shugaba Xi ya yi wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)