in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar Financial Times ta yi sharhi don maraba da ziyarar shugaban Sin a Birtaniya
2015-10-20 13:38:07 cri
A jiya da dare ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin London na kasar Birtaniya, don fara ziyarar aiki a kasar a hukunce. Kafofin yada labaru na Birtaniya sun dora muhimmanci sosai game da wannan ziyara, inda jaridar Financial Times a sharhin da ta wallafa, ta yi na'am tare da yaba wa matakan da Birtaniya ta dauka, na shirya gaggarumin biki don maraba da ziyarar da shugaban kasar Sin ya kawo.

A cikin sharhi, an ce, muhimmancin ziyarar ba zai tsaya kan gaggarumin biki da aka shirya ba, kuma ba zai tsaya kan yarjejeniyoyin ciniki da za a daddale tsakanin wadanda suka rufawa shugaban Sin Xi Jinping baya zuwa da kasar Birtaniya ba, ziyarar ta nuna cewa, Birtaniya ta sake fara gyara dangantakar da ke tsakaninta da sauran manyan kasashe a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China