in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan motar 'yan sanda a Kenya
2016-06-21 11:16:51 cri
A safiyar jiya Litinin 20 ga wata, wasu dakaru masu dauke da makamai sun kai hari kan wata motar 'yan sanda a gundumar Mandera dake arewa maso gabashin Kenya, wanda ya haddasa mutuwar 'yan sanda 5.

A wannan rana, kakakin 'yan sandan Kenya ya bayyana wa kafofin yada labarai cewa, an kai wannan hari, a lokacin da motar 'yan sanda ke ba da kariya ga wani bas da ya tashi daga Nairobi, hedkwatar kasar zuwa gundumar Mandera. 'Yan sanda 5 dake cikin motar sun mutu sakamakon yin musayar wuta da dakarun, yayin da wasu 'yan sanda 4 suka jikkata. Maharan ba su kai harin kan bas din ba.

A wannan rana, jami'in dake shiga tsakani a yankin arewa maso gabashin Kenya, Mohamed Saleh ya bayyana wa kafofin yada labarai cewa, dakarun sun kai hari a yankin dake kusa da iyakar kasar Somaliya. Ya ce, mai yiwuwa wadannan dakaru sun fito daga kungiyar Al Shabaab mai tsattsauran ra'ayi ta Somaliya.

Kafin wannan, an taba kai harin boma-bomai kan motar 'yan sanda a gundumar Mandera, yayin da 'yan kungiyar Al Shabaab suka yi garkuwa da motar safa safa da sauransu. Mr. Mohamed Saleh ya ce, wannan ne dalilin da ya sa motar 'yan sanda ta ba da kariya ga bas din a wannan rana.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China