Taron UNCTAD da aka yi na wannan karo shi ne karo na farko, bayan da M.D.D. ta fidda shirin tsare-tsare da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci na 2030 a watan Satumbar bara. Haka kuma taron zai kasance kunshe da sakamakon da aka samu a yayin taron koli karo na 10 na ministoci na kungiyar cinikayya ta duniya WTO da babban taron sauyin yanayi na Paris, da taron kolin kan tattara kudade don samun bunkasuwa na duniya, kana taron zai samar da wani dandalin yin mu'amala ga shugabanni mahalartar taron.(Bako)