in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ONUSIDA: Kenya ta kasance misali wajen rigakafi da kulawa da cutar kanjamau
2016-06-01 10:13:57 cri
Tsarin MDD kan yaki da cutar kanjamau ko Sida (ONUSIDA) ya nuna yabo a ranar Talata ga kamfen rigakafi da kula da cutar Sida a kasar Kenya, dake amafanawa a cewar wasu hasashe ga zuwa kashi 6 cikin 100 na al'ummar kasar. Babban darektan ONUSIDA, Michele Sidibe, ya bayyana cewa kasar Kenya ta samu yabo sosai daga duniya bisa babban mataki da amsar da ta bayar yadda ya kamata kan cutar SIDA ta hanyar cikakkun tsare tsare na gano, kulawa da sanya ido. Kenya ta kasance misali wajen rigakafi da kulawa da SIDA. Tun daga shekarar 2015, ana ganin cewa kimanin mutane dubu 900 daga cikin miliyan 1.5 na 'yan kasar Kenya dake rayuwa tare da cutar Sida za su samu kulawa, in ji mista Sidibe. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China