Yanzu ana samun karuwar 'yan kasar Kenya dake zaune a birane, inda kashi 56 cikin dari na mazauna birane a kasar suna zaune a unguwannin matalauta, kashi 63 cikin dari na dukkan 'yan kasar suna samun ruwa mai tsabta, kana kananan yara 'yan kasa da shekaru 5 da ke mutuwa ya kai 49 cikin 1000, wanda ya wuce matsayin yankin Afirka baki daya na 45 cikin 1000. (Bilkisu)