Shugaba Kenyatta wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da fadar sa ta fitar a birnin Nairobi, bayan ganawar sa da ministan harkokin wajen kasar Equatorial Guinea Agapito Mba Mokuy, ya ce akwai bukatar kafa wata cibiyar nahiya, wadda za ta rika baiwa shuwagabannin Afirka horo game da dabarun bunkasa hadin kan kasashen nahiyar.
Ya ce kasar sa ta ci gajiyar irin wannan hadin kai, don haka take fatan daukar nauyin wannan cibiya, wadda za ta iya habaka harkokin siyasa da mulki a nahiyar.
Shugaban na Kenya ya kara da cewa, abun bakin ciki ne ganin yadda wasu daga masu tallafawa nahiyar ta Afirka ke amfani da dogaron da nahiyar ke yi kan irin wannan tallafi, wajen cimma muradun kashin kai, maimakon muradun al'ummar nahiyar.
Mr. Mokuy dai ya ziyarci birnin Nairobi ne a ranar Lahadi, domin isar da sakon musamman na shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo. (Saminu)