in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Kenya sun yi amfani da barkonon tsofuwa domin tarwatsa masu zanga zanga
2016-05-17 10:30:26 cri
'Yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da barkonon tsofuwa a Nairobi, babban birnin kasar kan wani taron gangami na shugabannin 'yan adawa da magoya bayansu, da suka mamaye tituna domin yin allawadai da hukumar zaben kasar. Tsofon faraminista Raila Odinga, tsofon mataimakin shugaban kasa Kalonzo Musyoka, da tsofon ministan harkokin wajen kasar Moses Wetangula sun kasance masu shugabantar wannan zanga zanga da ta koma wani tashin hankali a gaban ginin hukumar zabe. Shugabannin adawar na bukatar ganin hukumar zabe mai zaman kamanta game da zabuka da iyakoki (IEBC), da aka dora ma nauyin shirya zabuka masu zuwa ta yi murabus. 'Yan adawar na zarginta da nuna son kai da kuma fifita shugaba mai ci, mista Uhuru Kenyata. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China