Hukumar MDD mai lura da 'yan gudun hijira ko UNHCR, ta nuna cewa kawo yanzu ba a kai ga tantance hakikanin halin da garin na Bosso ke ciki ba, bayan aukuwar hare-haren ranekun 3 da 5 da kuma 6 ga watan nan na Yuni.
Da yake yiwa manema labarai karin haske game da lamarin, Stephane Dujarric ya ce a kalla mutane 50,000 ne ake zaton sun tsere daga yankin, yayin harin karshe da mayakan na Boko Haram suka kaddamar a ranar Jumma'a.
Wasu kafofin watsa labarai na cewa yawan sojojin Najeriya da na Nijar da 'yan Boko Haram din suka hallaka a Bosso, yayin dauki ba dadin na ranar Jumma'a ya kai 30.
Yanzu haka dai hukumar UNHCR ta ce za ta yi aiki da sauran masu ruwa da tsaki a yankin, domin tallafawa wadanda ke gudun hijira. Hukumar ta kuma bayyana matsalar tsaro, da rashin kyakkyawar damar shiga yankunan jihar ta Diffa, a matsayin dalilan da suke dakile ayyukan jin kai a yankin. (Saminu Hassan)