Shugaban Sin da matarsa sun nuna alhini ga mutanen da suka mutu a sakamakon harin bom da aka kaiwa ofishin jakadancin Sin dake Yugoslavia
A jiya ranar 17 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping da matarsa Peng Liyuan sun isa birnin Belgrade da fara kai ziyara a kasar Serbia. Da farko dai, sun tashi zuwa tsohon wurin ofishin jakadancin Sin dake Yugoslavia da aka lalata, tare da nuna alhini ga mutane uku wato Shao Yunhuan, Xu Xinghu da Zhu Ying da suka mutu a sakamakon harin bom da aka kai wa ofishin. Shugaban kasar Serbia Tomislav Nikolić, shugabar majalisar dokokin kasar Maja Gojkovic da firaministan kasar Aleksandar Vučić sun halarci bikin.
Shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, za su cigaba da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu, kana bangarorin biyu za su yi kokarin samun ci gaba da zaman lafiya tare.
A ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 1999, kungiyar NATO dake karkashin jagorancin kasar Amurka ta kai hare-hare ga kawancen Yugoslavia, da kai harin bom kan ofishin jakadancin Sin dake kasar, wanda ya haddasa mutuwar dan jaridar kamfanin dillancin labaru na Xinhua Shao Yunhuan, da 'yan jaridar Guangming Xu Xinghu da Zhu Ying da suke aiki a ofishin jakadancin a lokacin, tare da jikkata mutane fiye da 10.(Zainab)