Jiya Jumma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Serbia Tomislav Nikolić a birnin Belgrade.
Shugaba Xi da uwargidansa Peng Liyuan sun samu tarbo daga wajen shugaba Nikolić da uwargidansa Dragica Nikolic, kuma shugaba Xi ya nuna godiya ga gwamnatin Serbia da jama'ar kasar saboda zumuncin da suka nuna musu.
A yayin shawarwarin, shugaba Xi ya nuna cewa, kasarsa na mayar da hankali sosai kan zumuncin gargajiya tare da kasar Serbia, da kuma yanayi mai kyau da dangantakar dake tsakaninsu ke ciki wajen samun ci gaba. Xi ya kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su yi tsayin daka kan girmama juna, da zaman daidai wa daida, da neman samun moriyar juna da samu nasara tare, kana da karfafa dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, tare kuma da kara habaka hakikanin hadin kai a fannoni daban daban, don zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.
A nasa bangare, shugaba Nikolić ya nuna yabo sosai kan babbar nasara da kasar Sin ta samu wajen raya zaman gurguzu, da yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen ketare, ya kuma bayyana cewa, kasar Serbia ta yi farin ciki matsayinta na dadadar abokiyar kasar Sin ta ainihi, ya kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su nuna goyon baya ga juna kan babbar moriya da batutuwan da suke mai da hankali a kai. Kasarsa kuma na fatan yin kokari tare da Sin, don ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba. (Bilkisu)