in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Najeriya sun taya juna murnar cika shekaru 45 da kulla dangantaka
2016-02-12 11:15:13 cri
A ranar 10 ga wannnan wata na Fabrairu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama, sun aike da sakonnin taya juna murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Wang ya ce, tun daga lokacin da aka kulla dangantaka tsakanin kasar Sin da Najeriya shekaru 45 da suka gabata, kasashen biyu ke ci gaba da mutunta juna tare da ziyartar juna domin kara karfafa dangantaka da yin musayar dabaru irin na zamani wanda hakan ya kasance abin misali ta fuskar cin moriyar juna a tsakanin kasashe masu tasowa. Kasar Sin ta dauki dangantakar dake tsakaninta da Najeriya a matsayin batu dake da matukar muhimmancin gaske, kuma a koda yaushe, a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Najeriyar musamman wajen aiwatar da kudurorin da aka cimma a lokacin taron karawa juna sani na dangantakar Sin da Afrika FOCAC da aka gudanar a karshen shekarar da ta gabata a birnin Johnnesburg na kasar Afrika ta kudu, inda kasar Sin ta yi amana cewar, aiwatar da wadancan kudurorin zai taimaka wajen kara habaka ci gaba da samun karfafuwar dangantakar tsakanin kasar Sin da Najeriya.

A nasa bangaren Geoffrey, ya aike da sakon taya murna ga al'ummar Sinawa da gwamnatin kasar Sin, bisa samun wannan babbar nasarar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu wadanda aminan juna ne. Ya kara da cewar an samu gagarumin ci gaba a tsawon wadannan shekaru. A cewarsa, Najeriya za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da dorewa da kuma karfafa wannan muhimmiyar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China