A yau Litinin ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi maraba da ziyarar da madam Merkel ta kara kawowa nan kasar Sin, ya kuma yi murnar da nasarar shawarwarin da aka cimma tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Jamus karo na 4, tare kuma da samun sakamako mai kyau a yayin shawarwarin.
A nata bangare, Merkel ta bayyana cewa, kasar Jamus tana maraba da kasar Sin da ta taka muhimmiyar rawa kan harkokin duniya, tana kuma fatan yin cudanya tare da Sin kan muhimman batutuwan duniya da na shiyya-shiyya. (Bilkisu)