MONUSCO da sojojin DR Congo sun ceto yara sama da dubu 8 daga hannun kungiyoyin dake dauke da makamai
Tawagar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar demokiradiyar Congo(MONUSCO) tare da hadin gwiwar sojojin kasar Congo, sun yi nasarar ceto sama da yara dubu 8 daga hannun kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2009 zuwa ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2015.
Mai rikon mukamin shugaban ofishin tawagar ta MONUSCO da ke garin Goma Josiah Obat ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke jawabi a gabashin kasar yayin bikin ranar yaran Afirka ta kasa da kasa.(Ibrahim Yaya)