Fadan dai ya barke ne lokacin da dubban masu zanga-zanga da shugabanninsu ke yi musu rakiya suka nemi tsalakawa yankin gidajen jama'a da hukumomin kasar suka killace.Inda 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa masu zanga-zangar.
Magoya bayan 'yan adawar sun shirya zanga-zangar ce domin suna rashin amincewarsu da hukuncin baya-bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke na baiwa shugaba Jospeh Kabila iznin zama a kan mulki bayan karewar wa'adinsa har zuwa lokacin da za a shirya zaben shugaban kasa.(Ibrahim)