A cikin wata sanarwa ta ranar Asabar, mista Sidikou ya nuna cewa wadannan tashe tashen hankali na iya kasancewa sarkakiya wajen gudanar da shawarwarin siyasa da ake ganin za su iya taimakawa ga kama hanyar shirya zabuka.
Yawaitar ayyukan kai gaban kotu da kuma wasu sauran ayyuka dake rage fadadar dandalin siyasa zasu iya kara ruruta wadannan tashe tashen hankali da kara tura shawarwarin siyasa da shugaban kasar ya kira da babbar murya cikin mawuyacin hali, in ji shugaban Monusco.
A cikin wannan sanarwa, mista Sidikou ya yi kira da hukumomin Congo da su girmama matsayin kasa mai 'yanci da walwala kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar Congo ya tanada.
Shawarwarin siyasa tare da dukkan bangarori da kuma girmama kundin tsarin mulki ita ce hanya daya tak da zata taimakawa masu ruwa da tsaki na Congo da su fuskanci kalubaloli na yanzu cikin nasara, musammun ma wadanda suke da nasaba da shirya zabuka, in ji jami'in MDD.
Mista Sidikou ya yi kuma tunatar kamar yadda kuduri mai lamba 2277 na kwamitin sulhu, cewa MDD na goyon bayan aikin tsohon faraministan Togo Edem Kodjo, da kungiyar tarayyar Afrika ta zama a matsayin mai shiga tsakani domin daidaita wannan tattaunawar siyasa. (Maman Ada)