Wannan maci da ya soma daga unguwar Bandal, da hadewa a filin Verodrome de Kintambo, inda sakatare janar na jam'iyyar PPRD mai mulki, Henri Mova Sakani, ya dauki magana domin nuna godiya ga magoya bayansu da suka zo da dama domin nuna goyon baya ga Joseph Kabila.
An hadu domin nunawa duniya cewa suke da babban rinjaye na al'ummar dake bayansu, dake kuma bayan shugaba Joseph Kabila, in ji Henri Mova Sakani a dandali.
A cikin jawabinsa, mista Sakani yayi allawadai da halayyar 'yan adawa, da a cewarsa, suke taro a kasashen Turai domin yin zagon kasa ga jamhuriya maimakon su dawo su koma teburin shawarwari da shugaba Kabila ya kira.
Duk abin zagon kasa da za su yi, maganar gaskiya ita ce ba za a yi zabuka a wannan shekara a RD-Congo ba, in ji Henri Mova Sakani a gaban jama'a, kafin ya kara da cewa wannan maci ya nuna babban goyon jam'iyyu da al'ummar kasa suke nunawa shugaba Joseph Kabila. Zanga zangar ta gudana cikin lumana, mako guda bayan jam'iyyun adawa sun gudanar da ta su zanga zanga domin yin allawadai da matakin kotun tsarin mulki. (Maman Ada)