Ma'aikatar kiwon lafiya na gudanar da wani kamfe yin allura ta gama gari, da tuni aka kammala a babban birnin kasar da kuma a yanzu haka kuma ake gudanar da irin wannan kamfe a cikin sauran yankunan kasar. A cikin wata sanarwa ta kungiyar likitoci marasa kan iyakar kasa (MSF) da aka fitar a ranar Talata, mutane 48 aka tabbatar sun karbu da zazzabin na shawara tun karshen watan Febrairu a RD-Congo. Yawancin mutanen sun fito daga kasar Angola. (Maman Ada)