Manufar shirya zanga-zangar, da shugabannin 'yan adawar ke yi wa dubban magoya bayan nasu jagora dauke da tutocin jam'iyyunsu, ita ce, nuna rashin amincewarsu da hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke na baiwa shugaba Joseph Kabila damar zama a kan mulki fiye da karshen wa'adinsa, wato har zuwa lokacin da aka shirya wani sabon zaben shugaban kasa.
A baya-bayan nan hukumar zaben kasar mai zaman kanta wadda ke da alhakin shirya zabuka a kasar ta bayyana cewa, ba za ta iya shirya zabuka a karshen wannan shekara ba kamar yadda aka tsara,domin tana bukatar watanni 17 kafin ta sake sabunta rijistar masu zabe.(Ibrahim)