in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano yadda gwamnatin kasar Amurka take tatsar bayanai ta hanyar azabtarwa bayan lamarin ranar 11 ga watan Satumba
2016-06-17 19:41:20 cri
A kwanakin baya ne hukumar leken asiri ta kasar Amurka wato CIA a takaice ta sanar da wasu muhimman bayanai fiye da 50, inda a karon farko aka bayyana yadda gwamnatin kasar Amurka take tatsar bayanai ta hanyar azabtarwa bayan lamarin ranar 11 ga watan satumba, abubuwan da suka sanya mamaki kwarai.

Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta yi bayani a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Juma'a a nan birnin Beijing cewa, ana fatan kasar Amurka za ta binciki kanta, tare da daukar hakikanan matakai na daina munanan ayyukan da ta ke yi na keta hakkin bil Adama. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China