in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da takardar bayani kan cin gabanta a harkokin kare hakkin 'dan Adam a shekarar 2013
2014-05-26 11:17:25 cri

A ranar 26 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da takardar bayani kan cin gaba da Sin da samu a harkokin kare bil Adama a shekarar 2013, inda aka bayyana nasarorin da kasar ta samu a fannoni daban daban dangane.

Takardar ta bayyana cin gaba na Sin wajen tabbatar da kare hakkin bil Adam bi da bi, ciki har da kara daga matsayin zaman rayuwar jama'a da kara ba da tabbaci kan ikon zama da bunkasuwar jama'a, da kafuwar tsarin ba da tabbaci na zamantakewar al'umma, wanda ya fi girma a duk duniya. An tabbatar da inganta zaman rayuwar mazauna birane da kauyuka musamman mafiya fama da wahalhalu, an kara inganta tsarin dimokuradiyya da shari'a, inda karo na farko aka cimma matsaya game da zaben wakilan majalisar jama'ar kasar Sin bisa kaso daya tsakanin birane da kauyuka. An kuma kara kayyade iko, da daura babban yaki da cin hanci da rashawa, da ci gaba wajen samun siyasa mai tsabta.

Takardar ta ci gaba da cewa, a shekara ta 2013, Sin ta kara ciyar da tsarin shawarwari da dimokuradiyya gaba, an kuma samu tsarin dimokuridayya ga jama'a kai tsari yadda ya kamata, baya ga kuma samu sabon ci gaba wajen kafa tsarin tafiyar da harkokin kasa da inganta kwarewar hakan. Kazalika an kuma tafiyar da harkokin gwamnati bisa ka'idoji kuma a fili, an tabbatar da 'yancin jama'a wajen bayyana ra'ayoyinsu, da kawar da tsarin tilasta wa masu laifuffuka yin aiki, da daukar matakai daban daban don kada a yanke hukunci bisa kuskure, da tabbatar da ikon 'yan kananan kabilu, da raya sha'anin nakasassu cikin wani sabon wa'adi. Sa'an nan an kara kyautata halin da ake ciki don nakasassu su iya shiga zamantakewar al'umma bisa daidaito. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China