Da dama daga masu fashin baki na ganin zaman rayuwar jama'ar kasar Sin ya samu kyautatuwa, kuma sha'anin kiyayen hakkin bil Adama ma ya samu sabbin nasarori.
Mataimakin shugaban sashen Asiya da Afirka na jami'ar Moscow Andrey Karneev, ya ce yanayin kiyaye hakkin bil Adama da Sin ke ciki ya samu kyautatuwa sannu a hankali, kuma sakamakon saurin bunkasuwar ci gaban tattalin arzikin kasar, da karuwar matsayin zaman rayuwar jama'arta, da bunkasar biranen kasar sunya sa an samu karin ci gaba.
Ya ce yanzu jama'ar kasar Sin suna samun bayanan da suke bukatai, da hidimar jinya cikin sauki, kana yanayin zaman rayuwarsu ma ya samu babban sauyi, kuma an samu wadannan ci gaba ne bisa tushen kyautatuwar yanayin kiyaye hakkin bil Adama.
Shehu malami a ofishin nazarin harkokin kasar Sin dake jami'ar Hoseo ta kasar Koriya ta kudu Chun Kalim, ya bayyana cewa takardar bayyanan ta nuna ci gaba da kasar Sin ta samu, wajen inganta sha'anin hakkin bil Adama a shekarar da ta wuce, musamman ma a fannin kiyaye adalcin shari'a, inda aka rubuta wasu batutuwan shari'a da aka hukunta cikin kuskure, wannan ya nuna niyyar gwamnatin kasar game da inganta tsare-tsaren gudanar da harkokin kasa bisa doka, da kiyaye adalci cikin zamantakewar al'umma, ta yadda za a kara ciyar da bunkasuwar sha'anin hakkin bil Adama gaba. (Bilkisu)