in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kada a saka siyasa wajen hakkin bil Adam, in ji jami'in Sin
2016-03-03 09:55:30 cri

An bukaci a kawar da siyasa ko yin baki biyu wajen tafiyar da harkokin hukumar hakkin bil Adam ta MDD, ko kuma a yi amfani da hakkin bil adam wajen tsoma baki a cikin ikon kasashe.

Liu Hua, wakilin musamman a kan ayyukan hakkin bil adam daga ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin, wanda ya bayyana hakan lokacin taron hukumar hakkin bin Adam karo na 31, ya ce, har duniya tana fuskantar tashin hankali da talauci, kuma dukkan hakkokin bil adam na da nasaba da kudurorin kasashe duka.

Ya ce, dukkan kasashe manya ko kanana, masu arziki ko matalauta daidai suke da sauran kasashen duniya, yana mai bayanin cewa, akwai fiye da hanya daya ta mulkin kasa, don haka bukatun jama'a na da muhimmanci.

A cewar Mr Liu Hua, daidaito tsakanin sassa biyu na hakkin bil adam, tattalin arziki, walwala da al'adu, hakkin al'umma da na siyasa, duk ya kamata a ba su wannan muhimmanci.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China