Bisa labarin da aka bayar, an ce, wani babban jami'in rundunar sojan Amurka da ya bukaci a sakaye sunansa, ya bayyana a farkon watan Afrilu cewa, ma'aikatar tsaron Amurka tana duba yiwuwar tura karin sojoji na musamman zuwa Syria. Amma babu wata masaniya kan hakikanin yawan sojojin da za a tura.
Manazarta sun bayyana cewa, watakila taron da za a kira a makon gobe na da alaka da wannan batu.
Shugaban manyan kwamandojin soja na Amurka, Joseph F. Dunford ya bayyana a kwanan baya cewa, zai mika wani shirin kara tura sojojin Amurka zuwa Iraki ga shugaba Obama, domin taimakawa rundunar sojan Iraki wajen fuskantar hare haren da kungiyar IS ke kaiwa birnin Mosol.(Fatima)