Ma'aikatar tsaro ta kasar Amurka ta sanar a jiya Laraba cewa, an kammala ayyukan soja na mataki na farko don yaki da kungiyar IS, hadaddiyar rundunar soja dake bisa jagorancin kasar Amurka za ta dukufa kan murkushe wannan kungiya.
Kakakin ma'aikatar tsaro na kasar Amurka Steve Warren ya bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana cewa, hadaddiyar rundunar soja ta cimma nasarar aikin rage karfin kungiyar IS da kuma hana bunkasuwarta, a nan gaba, za ta cimma burin murkushe wannan kungiya da kuma taimakawa kungiyoyin dake adawa da kungiyar IS na kasashen Iraki da Syria wajen mamaye muhimman garuruwan da kungiyar IS ta kwace.
Steve Warren ya kara da cewa, a yayin da ake gudanar da ayyukan yaki da kungiyar IS na mataki na farko, an cimma nasarar mamaye kashi 40 cikin dari na fadin kasar da kungiyar IS ta kwace. A cikin ayyukan soja da za a shirya yi, hadaddiyar rundunar soja za ta taimakawa sojojin tsaro na kasar Iraki wajen mamaye garin Mosul dake arewacin kasar, tare da kebe birnin Laca, muhimmin cibiyar kungiyar IS dake arewacin kasar Syria. (Lami)