in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana tayi nasarar zuwa mataki na gaba a wasannin share fage na Africa U-20
2016-06-16 15:12:39 cri

Kungiya wasan Ghana ta 'yan kasa da shekaru 20 wato Black Satellites, ta doke takwararta ta Habasha da ci 4 da nema a zagaye na biyu a wasannin share fage na matasa 'yan kasa da shekaru 20, wasan wanda aka buga a filin wasa dake birnin Cape Coast.

Da farko dai kungiyar wasa ta Young Walias na kasar Habasha ta yi nasara da ci 2 da 1 a wasan farko da aka buga a Addis Ababa.

Dan wasan tsakiya Yaw Yeboah ya zara kwallo yayin da 'yan wasan gaba Dauda Mohammed da Evans Mensah suka zara ragowar kwalleye biyu, lamarin da ya baiwa kungiyar wasan nasarar tsallakawa mataki na gaba.

Yanzu dai kungiyar wasan ta Black Satellites zata kara da takwararta ta kasar Senegal a wasan karshe na share fagen.

Za'a buga wasan farko ne a karshe mako a ranakun 8 zuwa 10 ga wata Yuli a Dakar, sannan bayan makonni biyu a buga wasa na biyu a kasar Ghana.

Kungiyoyin wasanni 7 ne zasu fafata inda za'a tantance kungiyar wasan da zata halarci wasan cin kofin Afrika na 'yan kasa da shekaru 20 wanda kasar Zambiya zata karbi bakuncinsa a ranakun 26 ga watan Fabrairu zuwa 12 ga watan Maris na shekarar 2017.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China